Thursday 11 December 2025 - 19:50
Ku Yi Hattara Da Tarkon Tattaunawa

Hauza/Majalisar malaman Musulunci a Labanon, a cikin wata sanarwa bayan taron su na wata-wata, ta yi gargadin cewa ya kamata a yi hattara da tarkon abin da ake kira "tattaunawa".

A rahoton sashen fassarar Ofishin Yada Labaran Hauza, Majalisar Malaman Musulunci a Labanon, a sanarwar da ta fitar bayan kammala taron ta na wata-wata, ta gargadi cewa ya kamata a yi hattara da abin da ake kira 'tattaunawa', domin ko da yake a zahiri na tsaro ko tattalin arziki ne, amma a cikin manufofinsa siyasa ne da kuma hanyar daidaita alaƙa.
Majalisar ta jaddada cewa "Yanayinmu na Musulunci ne, kuma ba za mu taɓa yin wani abu na daidaita alaƙa ba (da Sahayoniya), domin daidaitawar ba ta cikin yanayinmu."

Sanarwar ta kara da cewa: "Ana kai wa al'ummar Musulmi hari mai yawa na farfaganda da yakin ruwan sanyi wanda sakamakonsa shi ne raunana ruhi da lalacewar tunani; har wasu ruhinsu ya raunana, suna nuna rauni,, sun mika wuya, kuma sun yi tunanin cewa mika wuya ga abokan gaban Sahayoniya da bin umarninsu zai iya ceton su daga zurfin faduwar da suka fada cikinta."

Sanarwar ta ci gaba da cewa: "Wannan yanayi sakamakon labaran ƙarya, karkatar da gaskiya, rahotannin ƙirƙira na hukumomin leken asirin yamma, gudanar da tarurruka da kashe biliyoyin daloli; tare da ƙirƙira ƙarya da kuma nuna girma waɗanda duk kokarin haka shi ne haifar da tsoro da firgici daga abokan gaba, a sabanin haka, suna nuna Musulmai a matsayin masu rauni."

Majalisar Malaman Musulunci ta sannan ta lurar: "A nan ne rawar mu zata fito; tsayawa tsayin daka domin tunkarar yan mamaya da ƙoƙarin korar su daga duk faɗin ƙasashen Larabawa da na Musulunci. Wadannan yan mamayan masu ƙwace, basu gaji da mamaye ƙasa ba kawai, har ma da mamaye zukata, hankali da rayuka."

Sanarwar ta ci gaba: "Muna neman kawar da kowane tasiri da alamar wannan mamaya kuma mu shafe alamun sa, ta yadda babu wani abin dogaro ko biyayya da ya rage, kuma a lokaci guda, muna alfahari da ainihin mu na Musulunci."

A ƙarshe, majalisar ta jaddada: "Mafita ita ce kawai fitar da yan mamayan, domin wadannan yan mamayan ba za a kawar da su da ƙarfin tattaunawa ba, sai da ƙarfin makamai."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha